Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sadal al-Balad cewa, kyakkyawar karatun da Khaled Ibrahim Thani dalibi dan Najeriya a jami’ar Azhar ya yi a irin salon Abdul Basit ya dauki hankulan mutane sosai.
An dauki wannan hoton bidiyon ne a yayin wani biki da gidauniyar Abul Ainin Charity da kungiyar tsofaffin daliban kasar Azhar suka shirya domin karrama wadanda suka lashe gasar kur’ani ta kasa da kasa ta Azhar.
A cikin wannan bidiyon, Khaled Ibrahim Thani yana karanta aya ta 9 zuwa ta 15 a cikin suratul Mubarak Israa kamar yadda Sheikh Abdul Basit yake karantawa: